Mike Akhigbe | |||||||||
---|---|---|---|---|---|---|---|---|---|
9 ga Yuni, 1998 - 29 Mayu 1999 ← Oladipo Diya - Atiku Abubakar →
1994 - 1998
ga Augusta, 1986 - ga Yuli, 1988 ← Gbolahan Mudasiru - Raji Rasaki →
Satumba 1985 - ga Augusta, 1986 ← Michael Bamidele Otiko (en) - Ekundayo Opaleye (en) → | |||||||||
Rayuwa | |||||||||
Haihuwa | Etsako ta Tsakiya, 29 Satumba 1946 | ||||||||
ƙasa | Najeriya | ||||||||
Mutuwa | 28 Oktoba 2013 | ||||||||
Karatu | |||||||||
Makaranta | Jami'ar Tsaron Nijeriya | ||||||||
Harsuna |
Turanci Hausa Pidgin na Najeriya | ||||||||
Sana'a | |||||||||
Sana'a | ɗan siyasa | ||||||||
Digiri | admiral (en) |
Okhai Michael Akhigbe (an haife shi a ranar 29 ga watan Satumba, 1946 - ya mutu a ranar 13 ga watan Oktoba, 2013)[1] ya kasance Mataimakin Admiral na Nigerian Navy[2] wanda ya yi aiki a zahiri a matsayin Mataimakin Shugaban Najeriya (a matsayin Babban hafsan hafsoshi) a karkashin shugaban mulkin soja na Janar Abdusalami Abubakar daga Yunin shekarar 1998 zuwa Mayu 1999,[3] lokacin da aka kawo karshen gwamnatin soja kuma aka maye gurbinsa da Jamhuriyyar Najeriya ta Hudu . Ya taba yin aiki a matsayin Babban Hafsan Sojan Ruwa, babban hafsan hafsoshin Sojan ruwan Najeriya daga shekarar 1994 zuwa 1998; Gwamnan soja na Jihar Legas daga shekarar 1986 zuwa 1988; da kuma Gwamnan Soja na Jihar Ondo daga shekara ta 1985 zuwa 1986.[4]