Miyar Afang | |
---|---|
miya | |
Kayan haɗi | waterleaf (en) , Okazi soup (en) , Manja, albasa, crayfish (en) , ruwa, naman shanu da kifi |
Tarihi | |
Asali | Najeriya |
Miyar Afang miyar kayan lambu ce da ta samo asali daga mutanen Ibibio na Akwa Ibom a Kudancin Najeriya. Suna raba wannan miya a maƙwabtansu mutanen Efik na Calabar, Cross River.[1][2] Abinci ne da 'yan Najeriya suka fi sani da shi da kuma wasu sassan Afirka. Ya shahara musamman a tsakanin Ibibio da mutanen Anang na Akwa Ibom. Efik na jihar Cross River sun ɗauki wannan abincin a matsayin wani ɓangare na al'adunsu.[3] Ana yin ta ne a gida da ma wasu lokuta a shagulgula kamar bukukuwan aure, maulidi, binnewa, biki da sauransu galibi a yankin kudancin Najeriya.[4] Miyar Afang tana da gina jiki sosai kuma farashin shirye-shiryen na iya daidaitawa bisa buƙatun iyali.