Muhammad Yunus (an haife shi a ranar 28 ga watan Yunin shekara ta 1940) masanin tattalin arziki ne na Bangladesh, Kuma ya kasance babban kasuwa, kuma babban siyasa, kuma shugaban jama'a wanda ke aiki a matsayin Babban Mai ba da shawara na biyar na gwamnatin wucin gadi ta Bangladesh tun daga takawas ga watan Agusta shekara ta alif dubu biyu da a shirin da hudu (2024). [1] An ba Yunus lambar yabo ta Nobel ta zaman lafiya a shekara ta alif dubu biyu da shidda (2006) don kafa Bankin Grameen da kuma gabatar da ra'ayoyin karamin bashi da karamin kudi.[2] Yunus ya sami wasu babban girmamawa da yawa ta kasa da kasa, ciki har da lambar yabo ta Shugaban Amurka a alif na dubu biyu da tara (2009) da lambar yabo na zinare a 2010.[3]