![]() |
Wannan mukalar bata da Reference (Manazarta) ko daya, ka taimaka ta hanyar samar da Manazarta daga littafi ko yanar gizo, duba wannan shafin domin samun masaniya akan yanda zaka samar da Reference (Manazarta) a cikin wannan mukalar.
![]() |
![]() | |||
---|---|---|---|
20 ga Afirilu, 1996 - 29 Oktoba 2006 ← Ibrahim Dasuki - Sa'adu Abubakar → | |||
Rayuwa | |||
Haihuwa | Dange Shuni, 20 ga Afirilu, 1926 | ||
ƙasa | Najeriya | ||
Mutuwa | Abuja, 29 Oktoba 2006 | ||
Yanayin mutuwa |
accidental death (en) ![]() | ||
Ƴan uwa | |||
Mahaifi | Siddiq Abubakar III | ||
Sana'a | |||
Sana'a | sarki |
Ibrahim Muhammadu Maccido ɗan Abubakar, (Haihuwa: 20 ga watan Afrilu shekarar ta 1928Rasuwa: 29 ga watan Oktobar shekarar ta 2006), wanda aka fi sani da Muhammadu Maccido, shi ne Sarkin Musulmi na 19 a kasar nigeria. Ya kuma kasance mataimaki na farko ga Siddiq Abubakar III (shekarar ta 1903–shekarar ta 1988) wanda ya kasance Sarkin Musulmi na tsawon shekaru 50. Maccido ya yi ayyuka da dama, na gwamnati a lokacin rayuwarsa kuma ya yi fice sosai a matsayin mai hulda da Shugaban kasar Nijeriya Shehu Shagari (mulki shekarar 1979 – shekarar ta 1983) har zuwa lokacin da sojoji suka yi juyin mulki suka kawar da Shagari daga mulki. Lokacin da mahaifinsa ya mutu a shekarar 1988, shugaban gwamnatin mulkin soji a Najeriya, Ibrahim Babangida ya nada Ibrahim Dasuki (mulki a shekarar ta 1985 – shekarar ta 1993) a matsayin sabon Sarkin Musulmi, shawarar da ta haifar da zanga-zanga mai ƙarfi a duk arewacin Nijeriya.
A shekarar ta 1996, Sani Abacha (shekarar 1993 – shekarar ta 1998), tsohon shugaban mulkin sojan Nijeriya 6, ya tumɓuke Dasuki daga muƙaminsa ya kuma naɗa Maccido sabon Sarkin Musulmi. An kuma naɗa Maccido a ranar 21 ga watan Afrilu shekarar ta 1996 kuma ya yi mulki daga matsayin na tsawon shekaru goma. Ya kuma yi amfani da mukamin don kokarin sasanta rarrabuwar kawuna a tsakanin al’ummar Musulmin arewacin Najeriya, da inganta alaka da sauran al’ummomin Musulmi, da rage rikice-rikicen kabilanci a cikin Najeriya. A ranar 29 ga watan Oktoba shekarar ta 2006, bayan ganawa da Shugaba Olusegun Obasanjo, Maccido ya mutu a hatsarin jirgin saman kamfanin jirgin sama na ADC Airlines Flight 53, tare da ɗansa Badamasi Maccido, yayin da suke komawa Sakkwato. Akuma n binne shi a Sakkwato tare da yawancin sauran Sarakunan na Sakkwato.