Muharram | |
---|---|
watan kalanda | |
Bayanai | |
Ƙaramin ɓangare na | sacred month (en) da watan Hijira |
Bangare na | Hijira kalanda |
Mabiyi | Zulhajji |
Ta biyo baya | Safar |
Muharram Ko kuma da (Larabci:مُحَرَّم muḥarram), watan daya kenan a kalandar Musulunci. Yana daga cikin watanni hudu masu alfarma a shekara. Kalmar Muharram na nufin Kauracewa.
Ranar goma ga watan shine ranar Ashura wadda Musulmi yan Shi'a ke daukar ta a ranar bakin ciki ta duniya yayin da su kuma Musulmai mabiya Sunnah kan yi Azumi a wannan ranar Saboda a Hadisi Ance Annabi Musa ya yi azumi a ranar domin samun nasara a bisa ga Fir'auna. Sannan kuma Annabi Muhammad yayi umarni akan mabiya Addinin musulunci da su azumci wannan rana da kuma ranar tara ga watan kafin ta, wadda yan shi'a ke kira da Tasu'a Kuma sun hakikance a ranar ne aka kashe Imami Haussaini.