| |
Yankuna masu yawan jama'a | |
---|---|
Ivory Coast da Ghana |
Nzema ƴan ƙabilar mutanen Akan ne kimanin 328,700, daga cikinsu 262,000 suna zaune a kudu maso yammacin Ghana kuma 66,700 suna zaune a kudu maso gabashin Cote d'Ivoire. A Ghana an raba yankin Nzema zuwa gundumomin zabe uku na karamar hukumar Nzema ta gabas kuma ana kiranta da Evalue Gwira, gundumar Ellembele da Nzema West, wanda kuma ake kira gundumar Jomoro ta Ghana. Harshensu kuma ana kiransa Nzima (a Ghana) ko Appolo (a cikin Ivory Coast).