Mutanen Yanzi

Mutanen Yanzi

Yankuna masu yawan jama'a
Jamhuriyar dimokuradiyya Kwango

Ƙabilar Bayanzi (ko Yan, Yanzi, Yansi) ƙabila ce a Jamhuriyar Demokradiyar Kongo waɗanda ke zaune a kudu maso yammacin ƙasar kuma sun kai kusan miliyan bakwai.

Yanzi suna magana da Kiyansi (ko Eyans), harshe a cikin dangin Bantu. Bangaren siyasa mafi girma shine sarauta, wanda akwai kimanin 120 a karkashin sarakunan gargajiya 3 wanda mafi shahara daga cikinsu shine sarki Kinkie ko Binkie wanda sabon jigon sa shine Mfum' ngol' ko Mfumu ngolo kamar yadda Turawa suka furta (wanda aka fassara da "babba ko sarki mai ƙarfi") daga yankin Kidzweme, kuma kwanan nan magajinsa Mfum' Ntwàl Moka Ngol' Mpat', masanin tattalin arziki wanda aka horar a Harvard.

Bayanzi suna gudanar da tsarin yara zasu kasance 'yan ahalin uwa, don haka yaro yana cikin dangin uwa.

Matafiya 'yan mulkin mallaka na Belgium sun fara cin karo da su ne a Bolobo da ke kogin Kongo, a matsayin 'yan kasuwa a sama da kasan kogin. Sun dauke su aiki daga 1883, da farko a matsayin masu gadi. Bayan haka, an tilasta wa Bayanzi yin aikin noman shukar kwakwar manja, daga baya kuma aka yi amfani da su a matsayin magatakarda ko masu fassara.


From Wikipedia, the free encyclopedia · View on Wikipedia

Developed by Nelliwinne