noma | |
---|---|
economic sector (en) da field of work (en) | |
Bayanai | |
Ƙaramin ɓangare na | agriculture and forestry (en) da cultivation (en) |
Bangare na | primary sector of the economy (en) da food system (en) |
Mabiyi | gathering (en) |
Lokacin farawa | 8 millennium "BCE" |
Yana haddasa | Gandun daji |
Karatun ta | Ilimin kimiyyar noma |
Tarihin maudu'i | history of agriculture (en) |
Uses (en) | arable land (en) da fresh water (en) |
Classification of Instructional Programs code (en) | 01.0000, 01.00 da 01 |
NCI Thesaurus ID (en) | C16270 |
Earliest date (en) | 15 millennium "BCE" |
Wannan mukalar bata da Reference (Manazarta) ko daya, ka taimaka ta hanyar samar da Manazarta daga littafi ko yanar gizo, duba wannan shafin domin samun masaniya akan yanda zaka samar da Reference (Manazarta) a cikin wannan mukalar.
. |
Noma Hausawa na masa kirari "Noma na duke tsohon ciniki, noma tushen arziki, kowa ya zo duniya kai ya taras"
Noma yana da kuma ma'anoni da dama kasancewar irin amfaninsa a fannoni daban-daban. To, amma dai a fassara mafi sauki, za mu ce, Noma wata hanyar sana'a ce domin samun abinci da kudin shiga. Haka zalika, noma wata babbar hanya ce ta samun karuwar tattalin arziki da al'ummai suka raja'a a kan ta. A kasar Hausa ko kuwa, noma shi ne babbar hanya ta samun haɓakar tattalin arziki. Da noma ne Hausawa suka fi samun kudin shiga da abinci da ma kayayyakin da ake sarrafawa a masana'anta kamar tufafi da sauransu. A wajen Hausawa musamman mazauna karkara noma ya zama kamar wajibi (dole) a wajen Kuma kowanne Bahaushe, musamman ma magidanci.
Kusan mu ce ma kowanne Bahaushe ya iya noma, ya kuma san yadda ake yin shi. Noma da Kiwo duk suna nufin abu daya ne a ma'anar da ilimin zamani ya samar.