![]() | ||||
---|---|---|---|---|
| ||||
Wuri | ||||
| ||||
Ƴantacciyar ƙasa | Najeriya | |||
Jihohin Najeriya | Kwara | |||
Ƙananan hukumumin a Nijeriya | Offa (en) ![]() | |||
Babban birnin | ||||
Yawan mutane | ||||
Faɗi | 166,600 (2022) | |||
• Yawan mutane | 347.08 mazaunan/km² | |||
Labarin ƙasa | ||||
Yawan fili | 480 km² | |||
Altitude (en) ![]() | 435 m | |||
Bayanan Tuntuɓa | ||||
Kasancewa a yanki na lokaci |
Offa karamar hukuma ce, dake a Jihar Kwara a Nijeriya. Kimanin mutane wajen 120,100 ke zaune a wannan garin.[1] Ansan garin da sana'ar su ta saqa da rini, Wanda suke amfani da kayan lambu rini Wanda ake samu daga indigo na gida da sauran shuke shuke.[2] Ansan garin Offa da noman dankalin turawa da masara. Wanda ya hadu yazama abinci mafi soyuwa mai mahimmanci agaresu wato su mutanen offa na asali.[3][4]shanaye, akwiyoyi da tinkiya suma suna tashe a wannan muhallin. Manyan addinin da ake yi a garin sune addinin musulunci, addinin kirista sae kuma addinin gargajiya.
Tsofaffin gargajiyan da aka San garin dashi shine kokawa. Tarihin arzikin garin Offa Yana tattare a wani littafin James Bukoye Olafimihan Mai ilimi Kuma fasto a littafin shi Mai suna"iwe itan Offa" ma'anar shi "littafin tarihin garin Offa".
Mutumin daya samarda Offa shine Olalomi Olofa-gangan; Dan sarki Mai jiran gadon Oyo Kuma ainihin zuri'a daga sarki Oranmiyan a garin Ile-Ife, alokacin 1395. Shi din rikeken mahauci ne sabida darajar iyawanshi amatsayin shi na maharbi. Offa shine ainihin hedkwata na garin Iboyo masuyin yarabanci a garin kwara da osun.[2]