![]() | |||
---|---|---|---|
![]() | |||
27 ga Yuni, 2022 - ← Tanko Muhammad | |||
Rayuwa | |||
Haihuwa | 22 ga Augusta, 1958 (66 shekaru) | ||
ƙasa | Najeriya | ||
Harshen uwa | Yarbanci | ||
Karatu | |||
Makaranta | Jami'ar Obafemi Awolowo | ||
Matakin karatu |
Bachelor of Laws (en) ![]() | ||
Harsuna |
Turanci Yarbanci Pidgin na Najeriya | ||
Sana'a | |||
Sana'a | Lauya |
Olukayode Ariwoola (an haife shi a ranar 22 ga watan Agusta shekara ta 1954) masanin shari'a ne ɗan Najeriya kuma mai shari'a na Kotun Ƙoli ta Najeriya wanda ke riƙe da muƙamin babban alƙalin alƙalai na Tarayyar Najeriya. A da ya kasance Alƙalin Kotun ɗaukaka ƙara ta Najeriya, sai kuma a ranar 22 ga watan Nuwamba, shekarar 2011, aka naɗa shi a benci na kotun ƙolin Najeriya a matsayin mai shari’a, wanda babban jojin Najeriya ya rantsar da shi.[1][2] An naɗa shi yana jiran amincewar Majalisar Dokoki ta ƙasa a matsayin babban Alƙalin Alƙalan Najeriya a ranar 27 ga watan Yunin 2022 bayan murabus din Alƙalin Alƙalan Najeriya Tanko Muhammad.[3][4][5][6][7][8]