Paul Kagame (furucci|kəˈ|ɡɑː|meɪ); an haife shi 23 ga watan Oktoba a shekara ta 1957) shi dan'siyasan kasar Rwanda ne, kuma tsohon shugaban sojin kasar ne. Shine Shugaban kasar Rwanda ayanzu, yazama shugaba tun a shekara ta 2000 bayan tsohon shugaba Pasteur Bizimungu yayi marabus. Kagame kafin zamansa shugaban kasa, ya taba zama kwammanda na yan'tawaye wadanda suka kawo harshen Kisan-kare dangi na Rwanda a shekarar 1994. Ayanzu a kasar yakasance jagora de facto a sanda yarike mukamin Mataimakin shugaban kasar Rwanda da kuma Ministan tsaro daga shekarar 1994 zuwa 2000. Ansake zaben sa shugaba a watan Augusta shekarar 2017 da sakamakon da yasamu kashi 99% na dukkanin kuri'un da aka kada, sai dai masu bincike sunyi korafi akan yadda aka gudanar da zaben.[1][2] He has been described as the "most impressive" and "among the most repressive" African leaders.[3]