Pramila Patten | |||||
---|---|---|---|---|---|
12 ga Afirilu, 2017 - ← Zainab Bangura
| |||||
Rayuwa | |||||
Haihuwa | British Mauritius (en) , 29 ga Yuni, 1958 (66 shekaru) | ||||
ƙasa | Moris | ||||
Sana'a | |||||
Sana'a | university teacher (en) , Barrister da official (en) | ||||
Employers | Majalisar Ɗinkin Duniya | ||||
Kyaututtuka |
gani
|
Pramila Patten (An haifeta ranar 29 ga watan Yuni shekara ta 1958). Barista ce 'yar Mauritius-British, mai fafutukar kare hakkin mata, kuma jami 'an Majalisar Dinkin Duniya, wanda a halin yanzu take aiki a matsayin Wakilin Majalisar Dinkin Duniya na musamman kan cin zarafin mata a cikin rikice-rikice da kuma mataimakin babban sakataren Majalisar Dinkin Duniya; an nada ta a shekarar, 2017. An kafa ofishinta da ƙudurin Majalisar Tsaro mai lamba, 1888, wanda Hillary Clinton ta gabatar da ita, kuma ta gaji Margot Wallström da Zainab Bangura.
Patten ta kasance memba a kwamitin Majalisar Dinkin Duniya kan kawar da wariya ga mata daga shekarar, 2003 zuwa 2017, kuma ita ce mataimakiyar shugabar kwamitin.[1]