Progressive Tailors Club, ya kasance wani nau'in fim ne na siyasa a Najeriya wanda Biodun Stephen ya ba da Umarni kuma Niyi Akinmolayan da Victoria Akujobi suka shirya. Taurarin shirin sunhaɗa da Beverly Osu, Uzor Arukwe, Funnybone, da Blessing Jessica Obasi tare da Rachael Oniga, Lizzy Jay, Adedimeji Lateef, da Bolaji Ogunmola a matsayin masu tallafawa a shirin.[1][2]
An ɗauki fim din ne a birnin Legas da kewayen Najeriya. An fara haska shi a ranar 29 ga Oktoba, 2021.[3][4]