![]() | |
---|---|
Rayuwa | |
Haihuwa | Maputo, 11 Nuwamba, 1995 (29 shekaru) |
ƙasa | Mozambik |
Sana'a | |
Sana'a |
boxer (en) ![]() |
Mahalarcin
|
Rady Adosinda Gramane (an haife ta a ranar 11 ga watan Nuwamba 1995) 'yar damben Mozambique ce.[1] Ta wakilci Mozambique a gasar Commonwealth ta 2018 da aka gudanar a Gold Coast, Australia. [2] A wannan shekarar, ta kuma shiga gasar damben duniya ta mata ta AIBA ta shekarar 2018 a birnin New Delhi na kasar Indiya.
Tsohon ɗan damben ƙasar Mozambique Lucas Sinoia ne ya gano Gramane, wanda ya gayyace ta don gwada wasanni kuma ya zama kocinta.[3]
A shekarar 2019, ta samu lambar azurfa a gasar ajin matsakaita na mata a gasar wasannin Afrika da aka gudanar a Rabat na kasar Morocco.[4]
A shekarar 2020, ta samu gurbin shiga gasar neman cancantar shiga gasar Olympics ta Afirka da aka yi a Diamniadio, Senegal don fafatawa a gasar bazara ta 2020 a Tokyo, Japan, inda ta fafata a matakin middleweight. [5] Zemfira Magomedalieva ta kawar da ita a wasanta na biyu.
<ref>
tag; no text was provided for refs named profile_commonwealth_games_2018