Rahoton Lafiya ta Duniya

Rahoton Lafiya ta Duniya
mujallar kimiyya
Bayanai
Farawa 1995
Laƙabi World Health Report
Muhimmin darasi global health (en) Fassara
Maɗabba'a Hukumar Lafiya ta Duniya
Ƙasa da aka fara Switzerland
Harshen aiki ko suna Turanci

Rahoton Lafiya ta Duniya ( WHR ), jerin rahotanni ne na shekara-shekara wanda Hukumar Lafiya ta Duniya (WHO) ke fitarwa. An fara wallafa shi a shekarar1995, Rahoton Lafiya na Duniya shine wallafin WHO na kan gaba. [1] Ana wallafa rahotannin a kowacce shekara daga 1995 zuwa 2008, sannan kuma a cikin 2010 da 2013. Ana samun rahotannin a cikin yaruka da dama, kuma suna samun tantancewa daga ƙwararru akan wani takamaiman batun kiwon lafiya na duniya, wanda ya shafi dukkannin ƙasashen da suke membobin ƙungiyar. [2]

Babban manufar WHO ita ce samar da muhimmman bayanai ga masu tsara manufofi, hukumomin ba da agaji, kungiyoyin kasa da kasa da sauran su don taimaka musu wajen yanke manufofin kiwon lafiya da suka dace da kuma yanke shawara akan tallafi. Duk da haka, rahoton kuma yana samun isa ga mafi yawan masu sauraro, kamar jami'o'i, 'yan jarida da sauran jama'a. Ana sa ran cewa duk wani ƙwararre ko kuma wanda ke da ra'ayi akan amuran kiwon lafiya na duniya, zai iya karantawa kuma yayi amfani da shi.

  1. World Health Organization: Publications
  2. World Health Organization: Alphabetical List of WHO Member States

From Wikipedia, the free encyclopedia · View on Wikipedia

Developed by Nelliwinne