Iri |
world day (en) ![]() aukuwa |
---|---|
Suna saboda | Hausa |
Validity (en) ![]() | 2015 – |
Rana |
April 26 (en) ![]() |
Wanda ya samar | Abdulbaqi Aliyu Jari |
Hashtag (en) ![]() | #RanarHausa da #HausaDay |
Ranar Hausa (Ko kuma #RanarHausa) da turanci Hausa Day, Rana ce da aka keɓance domin nuna muhimmancin harshen Hausa, da tattauna hanyoyin bunƙasa shi da kuma jawo hankali akan irin ƙalubalen da harshen yake fuskanta.[1][2] ,[3] an fara bikin farko a shafukan sada zumunta musamman ta shafin twitter da niyyar hada L1 da L2 na masu magana da harshen Hausa. An zaɓi ranar 26 ga watan Augusta domin tuna ranar da aka ƙirƙiro haruffan "ƙ" da "ɗ" da "ɓ" wanda babu su a haruffan Turanci.[4][5] A Yayin bikin na cika shekara 5, mutane fiye da 400,000 suka gudanar da bikin ta yanar gizo da wasu kasashen da Hausawa suke zaune a sassa daban daban na duniya irinsu Faransa, Amurka, Kamaru, Ghana, Nijar, da Najeriya, kuma a irin wanan rana hausawa na duniya na cika shafukan zumunta da da zantuttuka masu nuna Alfahari da yarensu, wasu wajajen sukan shirya bukukuwa a wanan rana.[6]