Ray Finch | |||
---|---|---|---|
1 ga Yuli, 2014 - District: South East England (en) Election: 2014 European Parliament election (en) | |||
Rayuwa | |||
Haihuwa | Liverpool, 2 ga Yuni, 1963 (61 shekaru) | ||
ƙasa | Birtaniya | ||
Harshen uwa | Turanci | ||
Karatu | |||
Harsuna | Turanci | ||
Sana'a | |||
Sana'a | ɗan siyasa | ||
Wurin aiki | Strasbourg da City of Brussels (en) | ||
Imani | |||
Jam'iyar siyasa | UK Independence Party (en) |
Raymond Finch (an haife shi ranar 2 ga watan Yuni, 1963) ɗan siyasan Biritaniya ne wanda ya yi aiki a matsayin memba na Majalisar Tarayyar Turai (MEP) ta Kudu maso Gabashin Ingila a tsakanin shekara ta 2014 zuwa shekara ta 2019.[1][2]
Ya kasance dan takara na hudu da aka bayyana a jerin sunayen jam’iyyar UKIP a mazabar Kudu maso Gabashin Ingila, an zabe shi a matsayin dan majalisar Tarayyar Turai bayan zaben ‘yan majalisar Turai da aka gudanar a shekara ta 2014.
Finch shi ne shugaban kungiyar UKIP a majalisar gundumar Hampshire, wanda ya tsaya takarar majalisar Turai.[3] Ya ajiye aikinsa na matsayin kansila a watan Janairun 2017 bayan nada shi a matsayin shugaban tawagar 'yanci da dimokiradiyya kai tsaye ta Burtaniya a majalisar Turai.[4]
A ranar 17 ga watan Afrilun 2019, Finch ya bar UKIP don komawa Jam'iyyar Brexit.[5] Ba a tsayar dashi matsayin dan takarar jam'iyyar Brexit ba a zaben 'yan majalisar Turai na 2019 ba, kuma ya bar takarar kujerar MEP na Brexit Party a ranar 26 ga Mayu 2019.