Rikicin makiyaya da manoma a Najeriya

Infotaula d'esdevenimentRikicin makiyaya da manoma a Najeriya
Iri rikici
Kwanan watan 1998 –
Wuri Tsakiyar Najeriya
Ƙasa Najeriya
Makiyaya a kan hanyar su ta zuwa yanki da yake da korayen ciyayi a Bosso kan hanyar zuwa Lagos, a 1960, da Dr Mary Gillham
fulani nakiyo a cikin gari, lamarin da ka iya haifar da rikici da mazauna garin

Rikicin makiyaya da manoma a Najeriya galibi ya shafi rikice-rikice ne kan albarkatun kasa tsakanin Fulani makiyaya galibi Musulmai da akasarinsu manoma Kiristoci a duk faɗin Najeriya amma lamarin ya fi ƙamari a yankin Tsakiyar Najeriya (Arewa ta Tsakiya) tun bayan dawowar mulkin dimokuradiyya a 1999. Haka nan an kai hare-hare a Arewa Maso Yammacin Najeriya kan manoma wadanda galibinsu Hausawa ne. Duk da yake rikice-rikicen yana da asali na dalilai na tattalin arziki da muhalli, ya kuma sami matakan addini da kabilanci. Dubunnan mutane sun mutu tun lokacin da rikicin ya fara. Al’ummomin da ke zaune a karkara mazauna yankin galibi ana fuskantar hare-hare saboda yanayin rauni. Akwai fargabar cewa wannan rikici zai ba zu zuwa wasu kasashen Afirka ta Yamma amma galibi hakan gwamnatocin yankin sun yi kasa a guiwa. Hare-hare a kan makiyaya sun kuma kai su ga ramuwar gayya ta hanyar kai hari ga wasu al'ummomin.


From Wikipedia, the free encyclopedia · View on Wikipedia

Developed by Nelliwinne