Sarauniya Daurama |
---|
Sarauniya Daurama Yanzu haka akwai babban zanen Macijiya nade da wuƙa a bakin rijiya a bangon ofishin babban sakataren Jihar Katsina, wanda yake nuni ga tarihin Sarauniya Daurama, wanda ya fi shekara dubu.[ana buƙatar hujja]
Sarauniya Daurama ta gaji sauran yan'uwanta mata wajen sarauta domin wancan lokacin mata ne suke sarautar masarautar. Ita ce ta tara (9) a cikin jerin mata da sukayi sarautar daura.[1]