![]() | |
---|---|
political movement (en) ![]() | |
Bayanai | |
Ƙasa | Jamhuriyar Afirka ta Tsakiya |
Séléka kungiyar yan bindiga ce da akayi a kasar Afirka ta Tsakiya.[1] Kungiyar ta kafa gwamnati a kasar ranar 24 ga Maris 2013.[2] Shugaban kungiyar shine Michel Djotodia. Djotodia ya aiyana kansa a matsayin shugaban kasar.[3] Mafi yawanci yan kungiyar Musulmai ne.
A watan Oktoban 2021, an tabbatar da sauraron tuhumar da ake yi wa tsohon mayakin Seleka Mahamat Saïd a gaban kotun manyan laifuka ta duniya (ICC). Ana tuhumar wannan tsohon mayaƙin da laifukan cin zarafin bil'adama da laifukan yaƙi da aka aikata a 2013 da 2014. Wannan shi ne karon farko da wani tsohon ɗan ƙungiyar Seleka ya fuskanci alkalan Kotun.