Tele Ikuru

Tele Ikuru
mutum
Bayanai
Jinsi namiji
Ƙasar asali Najeriya
Shekarun haihuwa 24 ga Faburairu, 1966
Wurin haihuwa Port Harcourt
Muƙamin da ya riƙe Deputy Governor of Rivers State (en) Fassara da Deputy Governor of Rivers State (en) Fassara
Ilimi a Jami'ar jihar Riba s
Ɗan bangaren siyasa Rivers State People's Democratic Party (en) Fassara
Kyauta ta samu Fellow of the American Society of Mechanical Engineers (en) Fassara

Telenyem Renner Ikuru (an haife shi ranar 24 ga watan Fabrairun 1966), wanda aka fi sani da Tele Ikuru, injiniyan Najeriya ne kuma dan siyasa. An fara zaben shi mataimakin gwamnan jihar Ribas a cikin shekarar 2007 akan tikitin PDP tare da Gov. Celestine Omehia.[1] Bayan kotu ta soke zaben Omehia a waccan shekarar, an zabe shi a karkashin Chibuike Amaechi kuma aka sake zaben shi ofis a cikin shekarar 2011.[2]

Ikuru na cikin jami’an jihar da suka koma jam’iyyar All Progressive Congress tare da Gov. Amaechi a cikin shekarar 2013. Daga baya ya koma jam’iyyar People’s Democratic Party a ranar 22 ga watan Maris din 2015.[3]

  1. https://books.google.com.ng/books?id=hQzXzZfHV7QC&redir_esc=y
  2. https://www.coren.gov.ng/index.php?option=com_content&view=article&id=33
  3. https://web.archive.org/web/20150323063348/http://www.punchng.com/news/amaechis-deputy-ikuru-defects-to-pdp/

From Wikipedia, the free encyclopedia · View on Wikipedia

Developed by Nelliwinne