Tsarin Darasi | |
---|---|
Bayanai | |
Ƙaramin ɓangare na | planning (en) |
Bangare na | koyarwa |
Facet of (en) | didactic method (en) |
Tsarin darasi, shine cikakken bayanin malami kan darasin koyarwa ko “yanayin koyarwa” na karatu. Malami yana tsara jadawalin darasi na yau da kullum don jagorantar koyar da dalibai. Bayanai kan bambanta dangane da fifikon malamin, darasain da ake nazari, da kuma buƙatun ɗalibai. Za a iya samun ka'idodi da makaranta suka gindaya dangane da jadawalin.[1] Jadawalin darasi wani tsari ne na musamman da malami ke bi don gudanar da wani darasi, wanda kuma ya kunshi manufa (abin da ɗalibai yakamata su koya), yadda za'a cimma wannan manufa (hanya, salo) da kuma hanyar auna fahimtar dalibai ( gwaji, takardar aiki, aikin gida da dai sauransu).[2][3]