Umuagwo gari ne da ke cikin ƙaramar hukumar Ohaji/Egbema (LGA) a jihar Imo a Najeriya. Yawancin al'ummar garin Kiristanci ne kuma masu jin harshen Igbo. Garin na kan kogin Otamiri daga Ihiagwa da nisan kilomita 26 kilometres (16 mi) daga Owerri akan titin birnin Fatakwal.[1][2] Eze Tony Oguzie, Shugaban Majalisar Sarakunan Gargajiya a shiyyar Orlu (Imo West), shi ne sarkin Umuagwo.[3]