Umunumo ( Igbo Umu Numo ) wani gari ne dake cikin ƙaramar hukumar Ehime Mbano a jihar Imo a Najeriya.[1] Umunumo ya ƙunshi manyan yankuna biyu: Ibeafor da Ibenkwo. Kowanne daga cikin waɗannan yankuna ya ƙunshi ƙauyuka biyar a jimlace guda goma a Umunumo. Ƙauyukan su ne Umuofeke, Umunagbala, Umuwosha, Umuokpara da Umuchima a cikin Ibeafor da Duru Na Okiri, Ofor Owerre Ofor Ama, Umuanunu, Eze Na Obom da Umuaro a cikin Ibenkwo.[2]