Uwargidan shugaban Najeriya | |
---|---|
position (en) da take | |
Bayanai | |
Ƙaramin ɓangare na | First Lady (en) |
Farawa | 1963 |
Ƙasa | Najeriya |
Applies to jurisdiction (en) | Najeriya |
Uwargidan shugaban Najeriya ko First Lady of Nigeria a turance, mace ce da ba zaɓar su ake ba, amman, sukan riƙe muƙamin uwargidan shugaban Najeriya idan miji ya zama shugaban ƙasa. Uwargidan shugaban kasa a halin yanzu ita ce Aisha Buhari wacce ta rike muƙamin tun ranar 29 ga Mayun shekarar 2015.[1]
Kundin tsarin mulkin Najeriya bai samar da ofishi ga uwargidan shugaban ƙasar ko kuma mai mukamin shugaban ƙasa ba. Sai dai kuma an ware kuɗaɗe da ma’aikata a hukumance ga uwargidan shugaban Najeriya tun bayan samun ‘yancin kai.[1] Uwargidan shugaban kasa tana jawabi ne da taken Mai girma Gwamna.