Gabatarwa | Rajistar account | Yadda ake gyaran Wikipedia | Yadda ake mahadar shafi | Bada madogarar bincike | Shafukan tattaunawa | Manufofin Wikipedia | Karin bayani |
Wikipedia insakulofidiya ce ta ilimi na hakika, don haka ya zama dole duk abinda aka sa a bada madogarar bincike, wato inda aka samo shi. Ita kuma madogarar bincike dole ne ta kasance sahihiya, wato kamar sahihan jaridu, litattafai, mujallu da ma wallafaffun insakulofidiya. Su sahihan madogarar binciken dole ne su tabbatar da aukuwar al'amarin ko kuma ikirarin, amma kuma ba za'a lwafo abunda suka rubuta ba kai tsaye, domin hakan zai zama satan fasaha. Sabbin mukaloli, ko kuma ikirarin da ke a cikin mukaloli idan aka kasa samo sahihiyar madogarar bincike akansu, to dole ne a goge su daga Wikipedia.