Yankin Gabashin Najeriya | ||||
---|---|---|---|---|
| ||||
Wuri | ||||
| ||||
Ƴantacciyar ƙasa | Najeriya | |||
Labarin ƙasa | ||||
Yawan fili | 76,145.65 km² | |||
Bayanan tarihi | ||||
Ƙirƙira | 1 Oktoba 1954 | |||
Rushewa | 27 Mayu 1967 | |||
Ta biyo baya | Jihar Gabas ta Tsakiya, Jihar rivers da South Eastern State (en) | |||
Bayanan Tuntuɓa | ||||
Kasancewa a yanki na lokaci |
Greenwich Mean Time (en)
|
Yankin Gabashin Najeriya, ta kasance wani yanki na gudanarwa a Najeriya, wanda ta samo asali daga yankin Kudancin Najeriya da turawa suka mulka a shekarar 1954. Babban birninta na farko itace Calabar. Daga baya aka mayar da babban birnin kasar zuwa Enugu kuma babban birni na biyu itace Umuahia. An raba yankin a hukumance a shekarar 1967 zuwa sabbin jahohi uku, jihar gabas ta tsakiya, jihar Rivers da kuma jihar kudu maso gabas. Gabas ta tsakiya tana da babban birninta a Enugu, wanda yanzu ke a cikin jihar Enugu.[1]
Yankin ta hada manyan kabilun na uku da na hudu da na biyar a jerin kabilun Najeriya da suka hada da Igbo da Ijaw da Ibibio. Wannan yanki daga baya ta zamo Biafra, wacce ta yi tawaye daga 1967 zuwa 1970.[2]