Yankin Mulkin Mallaka na Arewacin Najeriya | |||||
---|---|---|---|---|---|
| |||||
Take | God Save the King (en) | ||||
| |||||
Wuri | |||||
| |||||
Babban birni | Zungeru | ||||
Yawan mutane | |||||
Addini | Musulunci | ||||
Labarin ƙasa | |||||
Bangare na | Daular Biritaniya | ||||
Sun raba iyaka da | |||||
Bayanan tarihi | |||||
Mabiyi | Royal Niger Company (en) | ||||
Ƙirƙira | 1 ga Janairu, 1900 | ||||
Rushewa | 31 Disamba 1913 | ||||
Ta biyo baya | Mallakar Najeriya | ||||
Tsarin Siyasa | |||||
Tsarin gwamnati | constitutional monarchy (en) | ||||
Ikonomi | |||||
Kuɗi | pound sterling (en) |
Arewacin Nigeria ( Hausa : Arewacin Najeriya ) ta kasance wani yanki na Biritaniya wanda ya wanzu daga shekarar 1900 har zuwa shekarar 1914 kuma ta mamaye yankin arewacin ƙasar da yanzu ake kira Najeriya.
Yankin yana da fadin 255,000 square miles (660,000 km2) kuma ya hada da masarautun Daular Sokoto da wasu sassa na tsohuwar daular Bornu, wadda,aka ci a shekarar 1902. Babban Kwamishina na farko na yankin shi ne Frederick Lugard, wanda ya kori cinikayyar bayi da hare-hare na ƙabilanci kuma ya kawo tsarin gudanarwa da aka kafa ta da hukumomin gargajiya na yankin.
An kuma kawo ƙarshen yankin na mulkin mallakan turawa a ranar 1 ga watan Janairun shekarar 1914, lokacin da aka hade yankin da Kudancin Najeriya da kuma Legas, ta zamo lardin Arewa na Mulkin Mallakan na Najeriya.