| |
Jimlar yawan jama'a | |
---|---|
47,000,000 | |
Yankuna masu yawan jama'a | |
Benin, Najeriya, Togo, Ghana da Kanada | |
Harsuna | |
Yarbanci | |
Addini | |
Kiristanci, Musulunci da Addinin Yarabawa |
Yarbawa mutanen yankin kudancin Najeriya ne masu magana da harshen Yarbanci, a matsayin harshen, ko yaren gado; wato harshen uwa ko harshen haihuwa. Dukkan Yarabawan da ke duniya, sun fito ne daga kaka ɗaya rak; wato tushen su guda ne wanda shi ne Oduduwa.[1]
Ƙabilar Yarabawa, suna ɗaya daga cikin manya-manyan ƙabilun Afirka ta Yamma (Biobaku, babu shekara). Mutane ne masu son junansu da kuma haɗin kai a tsakanin su. Suna da zaman lafiya da kuma matuƙar karɓar baƙi bakin gwargwado.
Fitaccen masanin tarihi, Dakta Babatola a shekarar (2019) yana kuma da ra’ayin cewa samuwar daɗaɗɗe kuma tsararren shugabanci guda ɗaya tilo, mai tushe guda; Oduduwa, ƙarƙashin sarautar gargajiya shi ne abin da ya ƙara danƙon zumunci a tsakanin Yarabawa duk kuwa da fantsamuwar su zuwa wasu sassan Afirka da ke wajen Ƙasar Yarabawa da ma wasu sassan duniya.[2]
Washington (2016), da Ogunbado (2003), sun yi ƙiyasin cewa sama da mutane miliyan talatin ne suke magana da wannan harshe a ƙasashen Afirka da kuma Brazil. Ogunbado (2003) ya ƙara da cewa sannan kuma akwai mutane sama da miliyan ɗaya da suke magana da wannan harshe a ƙasashe irin su Cuba da Birtaniya da sauran su.[3]
Kenan, muna iya cewa a bias ƙiyasi yanzu akwai Yarabawa a duniya sama miliyan talatin ɗaya. Ile-Ife ce babbar hedikwatarsu a gargajiyance sannan kuma Ooni-Ife shi ne babban sarkinsu tare kuma da cewa Oduduwa shi ne kakansu wanda dukkan Yarabawa daga gare shi suka fito, (Lange, 1995; Babatola, 2019; Babalola, 2017).