Bamum ( Shü Pamom</link> [ ʃŷpǎˑmə̀m ]</link> ' , ko kuma Shümom</link> ' yare ne wanda kuma aka fi sani da Shupamem, Bamun, ko Bamoun, yare ne na Gabashin Grassfields na Kamaru, akwae masu magana da yaren kusan mutun 420,000. Yaren ya shahara saboda rubutunsa na asali wanda Sarki Njoya da da'irar fadarsa suka kirkira a cikin Masarautar Bamum a kusa da 1895. Mawaƙin Kamaru Claude Ndam ɗan asalin yaren ne kuma ya rera shi a cikin waƙarsa.