Yusuf Olatunji

Yusuf Olatunji
Rayuwa
Haihuwa 1909
ƙasa Najeriya
Mutuwa 1978
Sana'a
Sana'a mawaƙi da drummer (en) Fassara
Artistic movement Sakara music (en) Fassara
Imani
Addini Musulunci

Yusuf Olatunji, Shine wanda aka fi sani da Baba Legba ko kuma Baba L'Egbaa (an haife shi a shekara ta 1905 - ya kuma mutu a shekara ta 1978), [1] dan wasan gangar Sakara ne na Najeriya, wanda ya shahara da salon kidan sakara an haife shi ne a shekarar 1905 ko shekarar 1906 a wani kauye da ake kira Gbegbinlawo a jihar Ogun a kudu maso yammacin Najeriya, kodayake har yanzu akwai shakku game da inda aka haife shi. A tsakiyar rayuwar sa ya shiga Musulunci ya kara masa shahara a sana'ar sa ta waken Yorubanci . An haife shi kirista kuma ya fito daga Iseyin a jihar Oyo . An san shi da suna Joseph Olatunji. Ya fara aiki a shekarar 1937 tare da rikodin sa na farko kuma ya shiga kungiyar Abibu oluwa a shekara ta 1927.

Ya mutu a ranar 15 ga watan Disamban, shekara ta 1978. Ya mutu yana da shekara 74. Ya bar ‘ya’ya guda 4 da mata 3. Olatunji aboki ne ga marigayi Lamidi Durowoju, marigayi Jimoh Ishola, wanda daga baya aka rataye shi a karshen shekarun 80s,Marigayi Raji Orire, Marigayi Badejo Okunsanya da sauran manyan mutane. Su ne mawadatan maza waɗanda galibi yayi wa waƙa. Ya kuma rera wakokin yabo da yawa ga wasu shahararrun kungiyoyin kula da jin dadin jama'a a yankin Kudu maso Yammacin Najeriya. Wata mace mai kudi da aka fi sani da suna Alhaja Kuburatu Abike Adebisi da aka fi sani da cash Madam a Abeokuta ta tura shi ƙasar waje don yi masa tiyata, ya mutu shekaru 7 bayan haka.

  1. Abiodun Salawu, "Reeling Nostalgia: ‘Aremote’ and the Enduring Sakara Music in Nigeria", Journal of Global Mass Communication, Vol. II, Nos. 1/2 (Winter/Spring 2009), p. 114.

From Wikipedia, the free encyclopedia · View on Wikipedia

Developed by Nelliwinne