![]() | |
---|---|
![]() | |
Bayanai | |
Gajeren suna | ZANU–PF |
Iri | jam'iyyar siyasa |
Ƙasa | Zimbabwe |
Ideology (en) ![]() |
African nationalism (en) ![]() ![]() ![]() ![]() ![]() |
Political alignment (en) ![]() |
left-wing (en) ![]() |
Harshen amfani | Turanci |
Mulki | |
Shugaba | Emmerson Mnangagwa |
Sakatare |
Obert Mpofu (en) ![]() |
Hedkwata | Harare |
Tarihi | |
Ƙirƙira | 22 Disamba 1987 |
Wanda ya samar | |
Mabiyi |
Zimbabwe African National Union (en) ![]() |
Ta biyo baya |
National Patriotic Front (en) ![]() |
zanupf.org.zw |
Zimbabwe African National Union - Patriotic Front (ZANU-PF) ƙungiya ce ta siyasa wacce ta kasance jam'iyyar Zimbabwe mai mulki tun bayan samun ƴancin kai a shekarar 1980. Robert Mugabe ne ya jagoranci jam'iyyar shekaru da yawa, da farko a matsayin Firayim Minista tare da Zimbabwe African National Union (ZANU) sannan kuma a matsayin shugaban ƙasa daga shekara ta 1987 bayan haɗewa da Zimbabwe African People's Union (ZAPU) kuma ya riƙe sunan ZANU-PF, har zuwa shekara ta 2017, lokacin da aka cire shi a matsayin jagora.
A zaɓen majalisar dokoki na shekara ta 2008, ZANU-PF ta rasa iko da majalisa a karo na farko a tarihin jam'iyyar kuma ta yi sulhu da yarjejeniyar raba iko tare da jam'iyyar Movement for Democratic Change - Tsvangirai (MDC). ZANU-PF ta lashe Zaɓen shekarar 2013, inda ta samu kashi biyu bisa uku. Jam'iyyar ta samu rinjaye a Zaɓen shekarar 2018.
A ranar 19 ga watan Nuwamba na shekara ta 2017, bayan juyin mulki, ZANU-PF ta kori Robert Mugabe a matsayin shugaban jam'iyya, wanda ya yi murabus bayan kwana biyu, kuma ya naɗa tsohon Mataimakin Shugaban ƙasa asa Emmerson Mnangagwa a madadinsa.