Zabe a Najeriya | |
---|---|
aspect in a geographic region (en) | |
Bayanai | |
Ƙaramin ɓangare na | general election (en) |
Facet of (en) | zaɓe |
Ƙasa | Najeriya |
Zabuka a Najeriya nau'i ne na zabar wakilan gwamnatin tarayyar Najeriya da jihohi daban-daban a jamhuriya ta hudu a Najeriya. Tun shekarar 1959 aka fara zabe a Najeriya tare da jam'iyyu daban-daban . [1] Hanya ce ta zabar shugabanni inda ‘yan kasa ke da ‘yancin kada kuri’a kuma a zabe su. A shekarar 2023, 'yan Najeriya na shirin gudanar da zaben shugaban kasa da kimanin mutane miliyan 93.4 da suka cancanci kada kuri'a a fadin tarayyar kasar domin zaben ranar 25 ga watan Fabrairu.