![]() | |
---|---|
Rayuwa | |
Cikakken suna | Zachee Ama Orji |
Haihuwa | Libreville, 1960s (55/65 shekaru) |
ƙasa | Najeriya |
Harshen uwa | Harshen, Ibo |
Karatu | |
Makaranta | Jami'ar Najeriya, Nsukka |
Matakin karatu | Digiri |
Harsuna |
Turanci Harshen, Ibo Pidgin na Najeriya Faransanci |
Sana'a | |
Sana'a | darakta, jarumi da mai tsara fim |
IMDb | nm1310918 |
Zachee Ama Orji, Haifaffen Libreville, Gabon, a 1960, ɗan wasan kwaikwayo ne na Najeriya kuma darekta, furodusa kuma mai shirya fina-finai.[1]
Orji, ya kammala karatun digiri a Jami'ar Najeriya, Nsukka. Bayan ya girma a Kamaru, Benin da Togo yana jin Ingilishi da Faransanci sosai.[2] Fim ɗinsa na farko shine a cikin 1991, kuma yana da taken Zunubi ba bafara ba . A wata hira da ya yi da Nollywood Post, Orji ya bayyana yadda ya samu jagaba a fim din ba tare da an duba shi ba. Tun daga lokacin Orji ya fito a fina-finai,daban-daban kuma a yanzu ya zama fitaccen jarumin Nollywood .
Ya auri Ngozi Orji yana da ƴaƴa uku kuma yana zaune a Najeriya.
Zack Orji ya fara fitowa a matsayin darakta a shekara ta 2000, tare da fim ɗin mai suna WEB wanda ya fito da kansa da kuma ƴar wasan Ghana, Kalsoume Sinare . Fim ɗin ya lashe mafi kyawun fim ɗin haɗin gwiwa. a cikin kyaututtukan Ghana na 2001.