Zainab Shinkafi Bagudu (an haife ta ranar 27 ga watan Maris 1968) mai ba da shawara ce a kan cutar kansa ta duniya da ke da sha'awar lafiyar mata, [1] Wadda ta kafa Gidauniyar MedicAid Cancer Foundation, ta ba da shawarar wayar da kan cutar kansa ta hanyar ba da horo ga ma'aikatan kiwon lafiya, tana tallafawa tantancewa, ganowa da kuma magance cutar kansa ga marasa lafiya a Najeriya. [2][3][4][5][6] Ita ce mai ba da gudummawa / yar jarida a Jaridar Blueprint [7] har wayau Ita ce mai bayar da shawara ce ga likitan yara, jakadar Ƙungiyar Ciwon daji ta Duniya kuma darekta ce a Hukumar Kula da Ciwon daji ta Duniya (UICC). [8][9][10][11][12]