Zariya (Ko kuma da turanciZaria, sai kuma Zazzau sunan da ake mata lakabi da shi). Zariya gari ne dake cikin arewacin Najeriya, kuma karamar hukuma ce a jihar Kaduna, tana da iyaka da Funtuwa, babban birnin Kaduna, da kuma Igabi duka a cikin ƙasar Najeriya. A bisa ga ƙidayar jama'a na shekara ta dubu biyu da shida (2006), jimillar mutane dubu dari bakwai da sittin (700060) ne a garin Zariya, to amman daga bisani an kimanta yawan su a shekara ta dubu biyu da sha bakwai (2017), ga jimillar mutane miliyan daya (1000000). Birnin Zariya tana da kilomita dari biyu da sittin (260kms) ne daga garin Abuja, kilomita tamanin (80kms) ne daga Zariya, kilomita dari daya da sittin (160) ne daga Kano.[1] Garin Zazzau an saka masa suna ne daga Sarauniya Amina.[2]